Mene ne "gida"? Ga Sinawa, gida wuri ne na zama wanda ake iya samun kwanciyar hankali a ciki. Yanzu, dalibai da yawa na kasa da kasa dake karatu a nan kasar Sin suna jin dadi kan bambance-bambancen dake kasancewa da kuma saukin da ake samu a fannonin zaman rayuwa da karatu, wanda ci gaban al'ummar kasar Sin ke kawowa, suna iya kwantar da hankulansu da jin yadda gida yake a nan kasar ta Sin. Chen Jinning da ta fito daga kasar Cambodia ita ma daya ce daga cikinsu.
Malam Wu Qunbin, dan kasar Sin ne wanda ya fara koyar da harshen Sinanci a kwalejin Canfucius ta jami’ar Nnamdi Azikiwe dake birnin Awka a jihar Anambra dake kudu maso gabashin Najeriya. An kafa kwalejin Confucius din a watan Maris na shekara ta 2008, bisa hadin-gwiwar jami’ar Xiamen ta kasar Sin da jami’ar Nnamdi Azikiwe dake Najeriya......
Yanzu haka ana gudanar da muhimman taruka biyu na kasar Sin, wato taron majalisar ba da shawara kan harkokin siyasar kasar (CPPCC) da na majalisar wakilan jama’ar kasar (NPC). Inda ake fatan kammalawa a ranar 13 ga watan Fabrairun da muke ciki. A jawabinsa shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar yayin da yake halartar taron tattaunawa da tawagar wakilan lardin Jiangsu, a taron farko na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin (NPC) karo na 14......
An gudanar da bikin mika lambobin yabon hukumar hadin gwiwar wasan kwallon kafa ta duniya wato FIFA a birnin Paris na Faransa a ranar 27 ga watan Febrairu, dan wasan gaba kuma kyaftin din kungiyar kasar Argentina Lionel Messi ya cimma lambar yabo na gwarzon dan kwallon duniya na hukumar FIFA na shekarar 2022 ajin maza, kana kungiyar Argentina ta fi samu lambobin yabo a gun bikin a wannan karo.
A cikin shirin na yau, zan kai ku tashar jiragen ruwa ta Zhoushan dake garin Ningbo na kasar Sin, don mu duba yadda ake kokarin raya fasahohin zamani a can. Tashar Zhoushan ita ce tashar jiragen ruwa daya kacal a duniya, dake iya jigilar kayayyakin da nauyinsu ya wuce ton biliyan 1 a duk shekara. A shekarar 2022 da ta gabata, an yi jigilar kayayyakin da nauyinsu ya zarce ton biliyan 1.25 ta tashar Zhoushan, adadi mafi girma a duniya, kuma wani matsayi da tashar ta kare cikin shekaru 14 da suka gabata.